Malam Garba Muhammad(BUBE) |
A bangaren yadda harkan tattalin arzikin da aka shiga yayi tasiri a kan sana'ar wayar salula kuwa,Bube ya kara haske ne a yadda farashin wayoyin ya karu a can garin Ikko(Lagos) da kusan kashi ashirin zuwa talatin a inda hakan ya shafi farashin wayar a kasuwa.
Binciken da nayi dai,ya nuna babu wani tallafi da masu sana'ar wayar a bakin sakatariyar Haliru Abdu ko bobban kasuwar Birnin kebbi suka taba samu daga gwamnati ko wata hukumar tallafa wa masu kananan kasuwanci ko irin wandannan kungiyoyin masu zaman kansu.Duk da yake,masu sana'ar wayar a Haliru Abdu,suna da kungiya na taimakon juna a tsakanin su,ya kuma bayyana mini cewa,a can baya an taba bukatar cewa su bada sunayen su don tallafi daga gwamnati amma har yanzu shiru suka ji.
Bube ya bukaci gwamnati ta tallafa masu domin akwai masu karamin karfi a cikin harkar kasuwancin wayar inda yin hakan zai sa su iya rike kansu har ma su jawo kannan su da abokan arziki suma su sami madogara ga tallafa wa rayuwar su,wanda hakan zai taimaka wa gwamnati ta hanyar sa matasa su dogara da kan su marmakin jiran sai gwamnati ta ba su aikin yi.
wajen sayar da waya,titin Badariya sakatariyar Haliru Abdu |
Ina kira ga mai girma gwamnan jihar kebbi Senator Atiku Bagudu da cewa ya duba koken da wa'yannan 'yan jihar Kebbin suka yi kan tallafi da suke bukata daga gareta,to amma ta yaya gwamnatin zata taimaka ?...me kuka yi a kasa wanda zai nuna zahirancin ci gaba da kuka samu ta hanyar kungiyar taku kafin gwamnati ta shigo cikin tsarin ku,yaya amanar shugabancin ku,nassarori da aka samu ko wani ingantaccen ci gaba ?.
Tags:
LABARI