Matasa Sun Bankawa Ofishin ‘Yan Sanda Wuta A Zamfara







Wasu matasa a garin Magazu da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara sun afkawa ofishin ‘yan sandan yankin inda suka kona shi kurmus sakamakon rashin jitawar da ya shiga  tsakanin matasan garin da ‘yan sandan.
Matasan sun zargi ‘yan sandan da yin sanadiyyar mutuwar wani matashi mai suna  Ibrahim Muhammad a hannun ‘yan sandan bayan garkame shi da suka yi a ofishinsu.
Wani ganau da ya so asakaya sunansa ya bayyanawa LEADERSHIP HAUSA cewa, mutumin da ya rasu ‘yan sandan zarginsa ne da sace wayar sadarwa.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Zamfara Shehu Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce, hukumar za ta tsaurara bincike.
Daga Leadership Hausa

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN